China ta gargadi Amurka akan batun tekun Pacific

amurka da china Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Hu Jintao na China da Barack Obama na Amurka

Kafofin yada labarai na gwamnatin China sun ja kunnen Amurka da kada ta kuskura ta iza wutar fito-na-fito ta hanyar kara karfin sojinta a yankin tekun Pacific.

Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar, Xinhua, ya ce Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton, ta yi yunkurin yiwa China kofar rago ta fuskar diflomasiyya yayin doguwar ziyarar da ta kammala a nahiyar Asiya.

Kamfanin dillancin labaran ya kuma zargi Misis Clinton ta wuce gona da iri wajen sukar China ba tare da ta ambaci sunan kasar ba.

Yanzu haka dai Sakatariyar Harkokin Wajen ta Amurka, Hillary Clinton, tana kan hanayarta ta zuwa Masar inda za ta gana da sabon shugaban kasar, Mohammed Morsi, dan kungiyar Muslim Brotherhood.

Wakilin BBC a birnin Alkahira ya ce yayin tattaunawar da za ta yi da shugaban na Masar, Misis Clinton za ta so ta ji tabbacin cewa sabbin shugabannin za su kare tsarin dimokuradiyya da 'yancin dan Adam a kasar.

Karin bayani