Shugaba Karzai ya bukaci a binciki kashe wani dan siyasa

karzai
Image caption Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan ya ba da umarnin gudanar da bincike a kan harin kunar bakin waken da ya hallaka wani fitaccen dan siyasa a kasar.

Dan kunar bakin waken dai ya rungumi Ahmad Khan Samangani ne sannan ya tashi bam din da ke jikinsa lokacin da dan siyasar ke gaisawa da mahalarta daurin auren 'yarsa a lardin Samangan.

Mai magana da yawun sojan kurfau a yankin, Lahl Mohammad Ahmadzai, ya ce mutane fiye da ashirin sun mutu a harin

Mista Samangani dai tsohon kwamandan mayakan sa kai ne kafin ya zamo dan siyasa daga bisani.

Har yanzu ba a san wadanda suka kai harin da ya sanadiyyar mutuwarsa ba, amma kuma ana zargin wata kungiya mai suna Islamic Movement of Uzbekistan wato IMU da kai wannan harin.

Kungiyar Taliban ta nesanta kanta da wannan harin na konar bakin wake.

Karin bayani