An daure wani matashi kan yunkuri kashe Obama

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Amurka Barrack Obama

An yankewa wani matashi dan kasar Uzbekistan hukumcin daurin shekaru 15 a kasar Amurka saboda samun sa da laifin yunkurin kisan Shugaba Obama.

Masu Shigarda kara sun shaidawa kotu yadda Matashin mai suna Ulugek Kadrov ya tsara yin kisan bayan saduwa da wata kungiyar masu kaifin kishin Islama da ke kasar sa ta Uzbekistan ta kafar internet.

Kadrov dai ya amsa aikata a laifin a watan Febrairu.

Hukumomin kasar ta amurka dai sun ce mutumin mai shekaru ashirin da biyu ya samu sauyin tunani ne ta hanyar saduwa da wani mutun ta kafar internet, kuma sun yi imanin cewar yana yiwa wata kungiyar musulmi masu gwagwarmaya da ke kasar sa ta haihuwa wadda Amurkar ta saka cikin jerin kungiyoyin 'yan ta'adda ne aiki.

Hukumci

Alkalin Kotun wadda ke birnin Birminham a jahar Alabama Abdul kallon yace kotu ta yankewa Kadrov daurin watanni 188 bayan ya ya roki afuwa a yayin zaman kotun.

Ya dai kaucewa samun daurin rai-da-rai saboda ya baiwa hukuma hadin kai kuma ya amsa laifukkan zama bakon da bai da iznin zama kasa wanda ya mallaki makamai kuma yayi barazanar kashe shugaban kasar a yayin yekuwar neman a sake zabensa.

An dai kama shine a wani Otel dake Alabaman sa'adda ya sayi bindiga mai sarrafa kanta da kuma gurnati guda hudu daga wani jami'in gwamnatin da yayi shigar burtu ta mai sayar da makamai.

Ulugbek Kadrov dai ya isa Amurka ne a shekara ta 2009 domin yin karatun aikin likita a wata makaranta amma sai ya kasa samun gurbi saboda baya iya magana da harshen turanci yadda ya kamata.

Karin bayani