An baiwa Fulani wa'adi su bar yankunansu a Filato

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto,

Taswirar Najeriya mai nuna Jihar Filato

Hukumomi a Jihar Filato da ke arewacin Najeriya sun baiwa mazauna wadansu kauyuka umarnin su kwashe inasu-inasu su yi gaba cikin sa’o’i arba’in da takwas domin dakarun tsaro za su kai samame a yankin da nufin tunkarar wadanda suke zargi da aikata kshe-kashe na baya-bayan nan a jihar.

Kauyukan da hukumomin suka baiwa mazaunansu wa’adin dai sun hada da Manga, da Kakuruk, da Kuzeh, da Maseh, da kuma Shong Two, yayin da aka ja kunnen matsungunan da ke kusa, wadanda umarnin tashin bai shafe su ba, da su yi taka-tsantsan yayin da ake aikin sojin.

Malam Saidu Maikano na cikin Fulani na gaba-gaba da suka halarci taron da a lokacinsa hukumomin tsaron suka bayar da umurnin.

A cewarsa “[Wannan wani] abin da ba a taba yi ba ne ake so a fara.... Ai wannan maganar banza ce kawai aka gaya mana.... Wannan abin dai ba abin da ya fi shi sai dai Tashin Kiyama kawai”.

To sai dai kuma kakakin rundunr tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato, Kyaftin Salisu Mustapha, ya ce ba Fulani ne kadai mazauna kauyukan da aka ce su tashi ba, kuma su ba su ma yi la’akari da batun kabila ba wajen yanke shawarar.

Shi kuwa shugaban kungiyar matasan Berom ta kasa, Mista Francis Jamang, ya ce suna goyon bayan matakin matsawar zai haifar da zaman lafiya.

Umarnin na hukumomin tsaro dai ya zo ne bayan wani mummunan tashin hankali da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane kimanin dari a yankunan, kana wadansu manyan ’yan siyasa biyu ’yan kabilar Berom suka rasa rayukansu a lokacin binne wadansu daga cikin mamatan—su ne kuma manyan ’yan siyasa na farko da suka rasa rayukansu a tashe-tashen hankulan na Jihar Filato.