Ba za mu bari a hana mu aikinmu ba —sojin Masar

Hillary Clinton da Hussein Tantawi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sakatariyar Harkon Wajen Amurka, Hillary Clinton, da shugaban majalisar sojin Masar, Hussein Tantawi

Jagoran Majalisar Koli ta Sojin Masar ya ce sojojin ba za su taba bari ba wani ya hana su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na kare kasar.

Field Marshal Hussein Tantawi ya furta wadannan kalaman ne jim kadan bayan ganawrsa da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka, Hillary Clinton.

An bayar da rahoton cewa Misis Clinton ta jaddada cewa wajibi ne sojojin su tabbatar kasar ta koma bin tafarkin dimokuradiyya.

Da take zantawa da manema labarai bayan ganawrata da Filed Marshal Tantawi, Misis Clinton ta ce:

“Daya daga cikin dalilan zuwa na Alkahira shi ne isar da sakon cewa Amurka na goyon bayan hakkokin dukkan al'ummu, kuma muna goyon bayan dimokuradiyya, amma idan dimokuradiyyar ta zarta shirya zabe kawai ta kai munzalin da masu rinjaye ke kare hakkokin marasa rinjaye”.

Karin bayani