A Najeriya Adams Oshomole ya samu nasarar zabe

Image caption Shugaban Hukumar zabe Prof. Attahiru Jega

A Najeriya, Hukumar zabe mai zaman kanta ta ce Gwamnan Jihar Edo adms Oshomole na Jamiyyar can ce ya lashe zaben da akayi a Jihar ranar Asabar. Jamiyyu bakwai ne dai suka shiga zaben na gwamna a Jihar.

Idanu dai suna kan zaben saboda gumurzun da akai hasashe za ayi musamman da Jamiyya mai mulki a kasar wato Jamiyyar PDP.

Yanzu haka dai ana can ana ta shagulgulan murnar samun nasarar da Jamiyyar ACN ta samu a can Jihar Edo.