Shugabannin Sudan da Sudan ta kudu sun gana

Al Bashir da Salva Kirr

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Al Bashir da Salva Kirr

Shugabannin Sudan da Sudan ta Kudu sun yi ganawar farko tun bayan da kasashensu suka kusan gwabza yaki a bara.

Omar al-Bashir da Salva Kiir sun gana ne lokacin taron gamayyar kasashen Afrika a Addis Ababa, babban birnin Habasha.

Babu dai wani abu da aka baiyana game da tattaunawar sai dai a karo na farko shugabannin sun yi musabiha da juna bayan kammalawa.

Taron na kasashen Afrika dai ya bukaci kasashen biyu su daidaita tsakaninsu kafin cikar wa'adin biyu ga watan Agusta da majalisar dinkin duniya ta basu.

Kasashen dai na sabawa ne game da rikicin kan iyaka, da harajin sufurin man fetur, da kuma rabon basussukan da ake bin tsohuwar kasar Sudan kafin a raba ta biyu.