Gwamnatin Syria ta musanta amfani da manyan makamai a Tremsa

tremsa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harin da aka kai a kauyen Tremsa

Wani mai magana da yawun gwamnatin Syria, Jihad Makdisi, ya musanta cewa an yi amfani da jirage masu saukar ungulu da makaman atilare a harin da aka kai kan kauyen Tremsa, al'amarin da masu fafutuka suka bayyana da cewa kisan kare-dangi ne.

A cewarsa makamai mafi girma da aka yi amfani da su, su ne rokoki a abin da ya kira martanin sojoji a kan kungiyoyi masu dauke da makamai.

Mista Makdisi ya ce "wannan al'amari ba kisan kare-dangi ba ne; martani ne da sojoji suka mai da a kan kungiyoyi masu dauke da manyan makamai wadanda suka ki yarda da masalaha ta siyasa".

Masu sa ido na Majalisar Dinkin Duniya da suka je Tremsa sun ce sojojin Syria sun yi amfani da makaman atilare.

'Yarjejeniyar Geneva'

Kungiyar ba da agaji ta Red Cross ta ce a yanzu tana dauka cewa rikicin da ake fama da shi a daukacin kasar Syria ya fada karkashin tanade-tanaden yarjejeniyar Geneva (geneva Convention) wacce ta shata ka'idojin yaki.

Kungiyar ta ce a yanzu haka akwai abin da ta kira yakin da ba na kasa-da-kasa ba a fadin kasar ta Syria.

A da dai wurare uku ne kawai a kasar ta Syria suka fada cikin irin wannan aji.

Kungiyar ta Red Cross ta ce yarjejeniyar ta Geneva ta baiwa bangarorin da suke yaki dama su yi amfani da karfi daidai gwargwado, amma kuma ta tanadi hukunce-hukuncen aikata laifukan yaki.

Karin bayani