Za'a horas da dakarun sojin Nijar

Matsalar tsaro a Sahel Hakkin mallakar hoto
Image caption Matsalar tsaro a Sahel

Kungiyar tarayyar Turai ta dau matakin aikewa da kwararrun jami'ai Hamsin zuwa Jamhuriyar Nijar domin horos da jami'an kasar kan yaki da ta'addanci.

A yau ne kungiyar tarayyar Turan ta yanke wannan shawarar bisa kiran da hukumomin Nijar suka yi wa kasashen yammacin duniya na su taimaka musu, shawo kan matsalolin tsaro dake da nasaba da ta'addanci a yankin Sahel.

Kungiyar tarayyar Turai ta bayyana damuwarta game da bazuwar makamai da ta ce ana yi a yankin Sahel tun bayan yakin da akai a Libya dadin dadawa da wanda ke faruwa a kasar Mali.

Ko a makon da ya gabata hafsoshin kasashen yankin Sahel suma sun yi wani taro domin duba hanyoyin da zasu shawo kan matsalar tsaron da ta addabi yankin.

A 'yan watannin bayan nan kasar Nijar na fama da matsalar sacewa da kuma garkuwa da turawa 'yan kasashen waje domin samun kudin fansa.

Karin bayani