Clinton zata tattauna da gwamnatin Israila

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Hillary Clinton a Isra'ila

Sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka, Hillary Clinton na Isra'ila bayan da ta tattauna da shugabannin Masar.

Al'ummar Isra'ila dai na cikin halin dar dar bayanda masu kishin Islama su ka dare mulkin Masar kuma ana sa ran Mrs Clinton za ta karfafa musu gwiwar cewa sabon shugaban kasar, Muhammad Mursi zai cigaba da aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Isra'ila.

Ana kuma sa ran tattaunawar ta ta za ta duba batun shirin nukiliya na kasar Iran wadda ke barazana ga Isra'ila da kuma batun sulhu a gabas ta tsakiya wanda ke kwan-gaba-kwan-baya.

Hillary Clinton dai ta gana da sabon shugaban kasar Masar da kuma shugaban rundunar sojin kasar don samarda fahimtar juna kan wutr da ta kunno kai kan Majalisar kasar.

Karin bayani