Sojoji da Fulani a Pilato sun sasanta

Sojoji a Pilato
Image caption Sojoji a Pilato

A Najeriya, Fulani a wasu kauyuka biyar dake kananan hukumomin Riyon da Barikin Ladi a jahar Pilato, sun amince su fice daga wuraran, kafin wa'adin da jami'an tsaro na musamman a jahar suka basu na su fice daga yankunan.

Wannan dai ya biyo bayan zazzafar mahawara da aka tafka game da tashin nasu, bayan da suka ce basu zuwa ko nan da taki daya.

Tuni dai kungiyoyi sukai ta yi allawadai da wannan mataki da mahukuntan sojin suka dauka, suna mai cewa ya taka hakkinsu a zamansu na 'uyan kasa.

Sai dai kuma rundunar sojin ta musamman a jahar ta Pilato ta ce ta dau wannan matakin ne domin kare lafiyarsu da dukiyoyinsu, a wani mataki da suka ce zasu dauka dan zakulo mutanan dake kai hare hare a yankin.

Kuma sun ce su riga sun sama musu matsugunnan da zasu zauna na wucin gadi har zuwa lokacin da zasu kammala aikin nasu.

Karin bayani