Fashin jiragen ruwa ya ragu

Fashin jirgin ruwa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fashin jirgin ruwa

Hukumar dake sa ido kan sufurin jiragen ruwa ta duniya, ta ce an samu raguwar fashin jiragen ruwa a kan teku a watanni shidda na farkon bana.

Wakiliyar BBC ta ce, adadin hare hare a kan teku da aka bada labari a duniya tsakanin watan Janairu da Yuni 177 ne, wanda ke nuna matukar raguwa, in aka kwatanta da 266 , a bara a daidai wannan lokaci.

Hukumar ta ce baza dakarun mayakan ruwa na kasashen duniya dake sintiri a kan teku, da kuma kasancewar masu gadi dauke da makamai kan jiragen ruwa, sun sa an samu raguwar hare hare daga 'Yan fashin kan teku na Somalia.

Sai dai kungiyar ta yi gargadin cewa, a duk lokacin da 'yan fashin suka yi nasara hawa kan jirgi, karfin da suke amfani da shi a kan ma'aikatan jiragen ruwan ya karu, idan aka kwatanta da a baya.

Karin bayani