Fada na kara tsananta kusa da Damascus

Hakkin mallakar hoto f

Bisa dukkan alamu tashin hankalin da ake yi a Syria na kara kusantar tsakiyar Damascus, babban birnin kasar.

A karon farko an tura sojojin gwamnati da motocin yaki zuwa anguwar Midan, dake tsakiyar birnin.

A cikin kwanaki biyun da suka wuce, an yi ta samun artabu tsakanin dakarun gwamnati da mayakan 'yan tawaye a galibin anguwanin dake kudancin birnin.

A yau da rana ne ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ke korafin cewa, yunkurin da kasashen yamma ke yi na sa Rasha ta sauya manufofinta a kan Syria da cewa kokarin shafa ma ta kashin kaji ne.

Karin bayani