Amurka ta amince da maganin Truvada

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Amurka Barack Obama

Jami'an lafiya a Amurka sun amince da maganin rigakafin kwayar cutar HIV mai karya garkuwar jiki na farko a tarihi.

An dai amince duk masu hatsarin kamuwa da kwayar cutar da su yi amfani da maganin mai suna Truvada.

Sai dai hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurka tace za'a yi amfani da maganin ne tare da kororon roba da kuma gwajin kwayar cutar HIV akai-akai.

Cutar HIV/AIDs ko Tsida na ci gaba da barazana musamman a kasahen yankin kudu ga sahara a Nahiyar Afrika inda ake bukatar karin wayar da kan jamaa kan cutar.

Karin bayani