An zargi bankin HSBC da almundahana

Wani kwamitin majalisar dattawan Amurka ya zargi bankin HSBC na Birtaniya da bada dama a halasta kudin haram ta hanyar yin sakaci wajen aiwatar da dokoki da kuma wani lokaci tankwara ka'idojin hada-hadar kudi.

Shugaban kwmaitin Sanata Carl Levin yace, bankunan dake kawance da HSBC a kasashe kamar Mexico na samu damar bude asusun ajiya a Amurka ba tare da an tantancesu ba, kuma kwamitin yace, a wasu lokuttan ana tauye amfani da hanyoyin gano yadda masu aikata muggan laifuka ke yin hada-hadar kudi, kuma hakan ya baiwa kasar Iran damar yin hada-hadar biliyoyin dalar Amurka.

Sai dai tuni shugabannin bankin na HSBC suka ce, zasu nemi gafarar duk kuskuren da suka aikata.

Wannan dai na faruwa ne bayan a 'yan makonnin baya bankin Barclays shima na Birtaniya ya fuskanci zargin tauye kudin ruwa.