An kai hari da makamin roka a wata makarantar Islamiyya a Jos

jos Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Birnin Jos ta sama

Wani yaro dan shekaru goma ya rasu, bayan wani hari da aka kai da makamin roka a wata makarantar Islamiyya a birnin Jos dake arewa maso tsakiyar Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewar makamin rokar ya fada kan wani gini kusada makarantar bisa kuskure.

Mahukunta a makarantar sun ce yaron daya rasu, ba dalibinsu bane.

Wakilin BBC a Jos, Ishaq Khalid ya ce an kai harin ne a lokacin da dalibai ke zana jarabawa.

Jos birni ne daya dade yana fama da tashin hankali masu nasaba da addini da kabilanci.

Wakilinmu ya ce ba wannan bane karon farko da makarantar Nurul Islam ke fuskantar matsaloli.

A cewarsa, a makwannin da suke wuce a damke wasu suna kokarin dasa bam a kusada makarantar.

Jos itace babban birnin jihar Pilato, kuma tana kunsu da al'ummomin Musulmi da Kirista.

Kungiyar 'yan Boko Haram a baya ta dauki alhakin kai hari a wasu coci coci a Jos dama wasu gine ginen gwamnati.

A makon daya gabata ma, wasu 'yan siyasa sun gamu da ajalinsu lokacin da suka halarci jana'izar mutanen da suka mutu sakamakon fadan kabilanci a yankin.

Karin bayani