An fara rusa gidajen marasa galihu a Lagos

Wata maata da aka rusa gidanta a Makoko Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wata maata da aka rusa gidanta a Makoko

Rahotanni daga Jihar Lagos a kudu maso yammacin Nijeriya sun ce ana can ana ci gaba da rusa matsugunan marasa galihu a unguwar Makoko da ke birnin Lagos.

Mazauna unguwar sun ce an tilasta mu su barin gidajensu ba tare da samar mu su da wani wuri ba.

A jiya ne dai gwamnati jihar ta Lagos ta fara aikin rusa gidaje a unguwar da aka kiyasta cewa tana da mazauna dubu dari biyar.

Da dama daga cikin mazauna unguwar dai masunta ne, kuma sun kauro ne daga Jumhuriyar Benin da kuma Togo masu makwabtaka.

An dai taba nuna unguwar ta Makoko a cikin wani fim da BBC ta shirya a shekara ta 2010, mai suna Welcome to Lagos, wanda ya harzuka gwamnatin Nijeriya, tana mai zargin wadanda suka shirya fim din da cewa sun nemi su kaskantar da Nijeriya ne.