Yajin aikin alkalai a Nijar ya fara tasiri

Shugaban kasar Nijar, Muhammadou Issoufou
Image caption Shugaban kasar Nijar, Muhammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar, yau ne kungiyar alkalan kasar ta SAMAN ta fara wani yajin aiki na kwanaki 3 a duk fadin kasar, don matsa lamba kan gwamnati na ta biya musu wasu bukatunsu.

Alkalan dai na nemangwamnatin Nijar din ne da ta kyautata musu yanayin aikinsu ta hanyar sama musu isassun kayayyakin aiki.

Tuni dai yajin aikin ya fara yin tasiri kan harkokin jama'a, kuma ya zuwa yanzu gwamnatin ba ta ce uffan ba dangane da yajin aikin.

Karin bayani