Jami'in gwamnatin Syria ya koma ga yan adawa

Image caption Nawaf Fares, tsohon Jakadan Syria

Jami'in Syria mafi girma da ya koma goyon bayan masu adawa da gwamnatin kasar ya shaidawa BBC cewa mahukuntan kasar ne ke amfani da dakarun al-Qaeda wurin kai baki dayan manyan hare-haren bama-baman da ke haddasa asarar rayuka da dama.

Shugabannin Syria dai sun sha musanta alhakin kai harin bama-baman tare da zargin 'yan ta'adda da kai hare-haren.

Nawaf al-Fares wanda a makon jiya ya ajiye mukaminsa na Jakadan Syria a Iraqi ya kwatanta shugabannin Syria da kerkecin da aka jikkata wanda zai yi duk abinda zai iya domin tserar da ransa.

Nawef ya kara da cewa akwai bayanai da ba'a tabbatar ba cewa an dan yi amfani da makamai masu guba a garin Homs. Sai dai na acewarsa ya yi imanin gwamnatin ba za ta ki amfani da makaman masu guba ba matukar ta ga cewa al'ummar Syria na neman samun nasara a kanta.

Karin bayani