Mataimakin Firayim Ministan Turkiyya ya je Mogadishu

Bekir Buzdaq (a gefen dama) da Sheikh Sharif Sheikh Ahmad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mataimakin Firayim Ministan Turkiyya, Bekir Buzdaq da Firayim Minista Abdiweli Mohamed Ali na Somalia

Mataimakin Firayim Ministan Turkiyya, Bekir Buzdaq, ya kai ziyara Mogadishu, babban birnin kasar Somalia, inda ya bayar da sanarwar cewa kasarsa za ta gina ofishin kula da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na birnin.

Mataimakin Firayim Ministan na Turkiyya ya gana da Shugaba Sheikh Sharif Sheikh Ahmad na Somalia tare da Firayim Ministansa Abdiweli Mohamed Ali; sun kuma tattauna a kan ayyukan ci gaban da Turkiyya ke gudanarwa a kasar ta Somalia.

Mista Buzdaq ya shaidawa manema labarai cewa kasarsa za ta ci gaba da aikin da ta take yi a Somalia kuma ba tare da bata lokaci ba za ta fara aikin gina makarantu, da asibitoci, da sauran gine-gine a birnin.

“Muna ganin Somalia na bunkasa—a cikin kasa da shekara guda mun ga gagarumin sauyi.

“Mun ga yadda aka sake gina Mogadishu. Nan da wata guda mai zuwa za mu fara aikin sake ginin tituna da asibitocin Mogadishu”, in ji Mista Buzdaq.

Ya kuma kara da cewa, “Muna so mu kawo sauyi a Somalia nan take, mu kuma taimakawa Somaliyawa su yanke shawara da kansu a kan abin da suke so ba tare da tsoma bakin kasashen waje ba. Na tabbata wannan kasa za ta ci gaba cikin dan kankanin lokaci saboda himmar Somaliyawa”.

Shi kuwa Shugaba Sharif ya yaba ne da kokarin gwamnatin Turkiyya na taimakon Somaliyawa, sannan kuma ya bayyana jin dadinsa da yadda kasar ta Turkiyya ke samar da kudade don bunkasa ilimi da kuma baiwa dalibai daga Somalia gurbin karo ilimi a jami'o'in Turkiyya.

A cewar Shugaba Sharif, ”Mun tattauna a kan aikace-aikacen da Turkiyya ke gudanarwa na sake gina ma'aikatun gwamnati, da kungiyoyin farar hula da kuma taimakawa Somaliyawa ta hanyoyi daban daban. Sun shaida mana cewa a shirye suke su cika alkawuran da suka yi, har ma su dora a kai”.

Turkiyya dai ta yi uwa ta yi makarbiya a harkar sake gina Somalia.

Lokacin da kasar Somalia ta afka cikin matsalar karancin abinci bara ne dai gwamnati da kungiyoyin agaji na Turkiyya suka fara tattaro gudunmawa ga Somaliayawan da ke gujewa matsanaciyar yunwa ta hanyar sama musu abinci, da ruwa, da matsugunai, da kuma cibiyoyin kiwon lafiya.

A shekara ta 2011 Firayim Ministan kasar ta Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya kai ziyara Somalia tare da wata tawaga ta manyan 'yan kasuwa, da 'yan siyasa, da sanannun mutane.

Kasar ta Turkiyya ta kuma bude ofishin jakadancinta a Mogadishu, sannan a watan Maris na bana jiragen saman kasar suka fara zirga-zirga zuwa birnin na Mogadishu.

A bara kawai an kiyasta cewa Turkiyya ta baiwa Somalia agajin dala miliyan dari uku da sittin da biyar.