Bam ya halaka Isra'ilawa shida a Bulgaria

Motar da bam ya tashi a cikinta Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Motar da bam ya tashi a cikinta

Wani bam da ya tashi a cikin wata motar safa dauke da wasu 'yan kasar Isra'ila masu yawon bude ido a Bulgaria ya halaka mutane akalla shida, ya kuma raunata wadansu sama da talatin.

Jami'an Bulgaria sun tabbatar da aukuwar al’amarin a filin saukar jiragen sama na birnin Burgas dake gabar tekun Bahar Aswad.

Wadansu shaidu sun fada wa gidan talabijin na Isra'ila cewa wani ne ya shiga cikin motar bus din; shigarsa kuma ke da wuya sai aka ji tashin bam din.

Kakakin gwamnatin Amurka, Jay Carney, ya ce kasarsa ta yi Allah-wadai da irin wadannan hare hare a kan mutanen da ba su ji, ba su gani ba, musamman ma kananan yara.

Firayim Ministan Isra'ila , Benjamin Netanyahu, ya ce bisa dukkan alamu akwai hannun kasar Iran—ya kuma ce Isra'ila za ta mayar da martani mai karfin gaske.