Yan Kabilar Nasa a Colombia sun kori soji

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojan Colombia

Wasu kabiliu a kasar Colombia da ke Nahiyar Amurka ta Kudu sun ce sun kori kimanin sojoji dari daga sansanin da suke gadi a lardin Cauca da ke kudu maso yammacin kasar.

Dama dai 'yan kabilar Nasa sun baiwa sojojin wa'adin zuwa tsakar daren jiya su tashi daga sansanin.

Kabilun sun ce sun gaji ne da musayar wuta tsakanin sojin Colombia da kuma babbar kungiyar 'yan tawaye ta FARC wacce ke rutsawa da su akai-akai.

Sai dai rundunar sojin ta ce ta janye dakarunta na wucin-gadi domin kaucewa arangama da 'yan kabilar Nasa.

Karin bayani