Muna cikin kunci - Inji Fulani a Jihar Pilato

Taswirar Jihar Pilato
Bayanan hoto,

Taswirar Jihar Pilato

Rahotanni daga Jihar Filato a arewacin Najeriya sun ce al'umar Fulanin da hukumomin tsaro suka fitar daga gidajensu da nufin gudanar da aikin tabbatar da tsaro na ci gaba da kasancewa a cikin wani mawuyacin hali.

Hakan dai na faruwa ne duk kuwa da taimakon da hukumomin suka ce sun kaiwa Fulanin don saukaka musu kuncin da suka fama da shi.

A waje guda kuma wata kungiyar Fulani makiyaya ta nuna damuwa a bisa wuraren da aka ajiye Fulanin da aka fitar daga gidajensu a jahar Pilato don yin binciken zargin cewar akwai makwantar bata gari.

A wata takardar sanarwa da kungiyar ta rabawa manema labarai a Kaduna, kungiyar mai suna Pastoral Resolve a Turance, na ganin a yanzu Fulanin da ke zaune a makarantun Firamare hudun da aka jibge su na zaune ne cikin kunci.

A saboda haka ta yi kira ga rundunar ta hadin guiwar tsaron ta STF da ta hanzarta kammala ayyukan da ta ce za ta gudanar a yankunan Fulanin.

A wani bangare kuma wata kungiyar ta Fulani na ganin akwai wasu hanyoyin samar da zaman lafiya a jahar ta Pilato baya ga ta amfani da karfin tuwo da aka dade ana amfani da ita.

Ta ce kamata yayi dukanin wasu shugabannin al'uma su rinka hudubar samar da zaman lafiya ga jama'a maimakon maganganun da ka iya kara dagule lamura.