Mutane na fama da karancin kudi gabda azumin Ramadan

kano
Image caption Taswirar Najeriya

A yayin da musulmi a fadin duniya ke ci gaba da shirye shiryen azumin watan Ramadana, jama'a a jihar Kano na kokawa da karancin kudin da za su sayi kayan bukatun yau da kullum a cikin watan na azumin.

Karancin kudin da ke hannun mutanen dai ya sa suma 'yan kasuwar na kokawa da rashin ciniki, idan aka kwatanta da irin wannan lokaci a shekarun baya.

Hakan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar kididdiga ta Nigeria ke cewa farashin kayayyaki musmman ma kayan abinci ya tashi a watan da ya gabata.

Wasu daga cikin mutane da wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai, sun bayyana cewar basu da kudin da zasu sayi kayayyakin abinci ga azumi na gabatowa.

Karin bayani