An nuna damuwa kan rumbunan makamai da aka bude kan tekun Afurka

Jiragen ruwa a teku Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jiragen ruwa a teku

Wata kungiya ta majalisar dinkin duniya dake sa ido kan Somalia ta ce akwai wasu rumbunan makamai da aka bude kan tekun Afurka, domin su rika bada hayar makamai ga kampanonin tsaron dake kokarin magance matsalar fashi a kan teku.

Wakilin BBC ya ce, tsofin jiragen ruwa ne da ake amfani da su wajen jan jiragen da suka lalace ko samar da kayan aiki, ake amfani da su yanzu a matsayin rumbunan makaman da ake bada haya, a yankunan ruwan da babu wata kasa dake iko da su.

Rahoton majalisar dinkin duniyar na cewa idan ba an dauki matakan sa ido kan aikace aikacen kampanonin bada hayar makaman ba, za su iya yin barazana ga zaman lafiya, da kuma harkokin tsaro a yankin, maimakon su taimaka a rage fashin kan teku.