Dan kunar bakin wake ya kashe kusoshin gwamnatin Syria

syria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tashin hankali na kara muni a Syria

Gidan talabijin na Syria ya ce an kashe surukin Shugaba Assad, Assef Shawkat, wanda yake mai fada aji sosai, a wani harin kunar bakin wake da bam da aka kai a hedikwatar cibiyar tsaro ta kasa a Damascus babban birnin kasar.

Haka nan kuma an kashe Ministan tsaro, Daoud Rajiha, sannan kuma an raunata babban jami'in tsaron ciki na Syriar, Hisham Iktiar da Ministan cikin gida Mohammad Ibrahim al- Shaar.

Dan kunar bakin waken ya kai harinne a wani taron majalisar Ministoci na manyan jami'an tsaron kasar.

Gwamnatin Syriar ta maida martani kan harin, tana mai cewa a yanzu ma zata kara daukar tsauraran matakai a kan wadanda ta kira 'yan ta'adda, kana kuma ta zargi Isra'ila da Amurka da mara masu baya.

An kai harin ne yayinda fada ke kara kamari a birnin Damascus, inda ake jin karin amon tashin bamabamai.

Ana cewa wasu bamabaman sun tashi a hedkwatar rundunar soja ta hudu ta kasar ta Syria, wadda ke gadin fadar shugaban kasa.

'Allah wadai'

Sakataren harkokin wajen Birtaniya, William Hague ya la'anci harin kunar bakin waken da yayi sanadiyar mutuwar manyan jami'an Syriar biyu.

Hague yace "hare haren sun kara tabbatar da bukatar da ake da ita cikin gaggawa ta samun wani kuduri mai karfi na Majalisar Dinkin Duniya da zai kawo karshen rikicin kasar ta Syria".

Kafin haka Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya , Ban-Ki Moon ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya dauki mataki na bai daya kan rikicin Syriar, bayan wata ganawa da shugaban China, Hu Jintao, a birnin Beijing.

Karin bayani