Fulani sun koma gidajensu ba tare da izini ba

Taswirar Najeriya mai nuni da Jihar Pilato
Image caption Taswirar Najeriya mai nuni da Jihar Pilato

A Najeriya Hukumomi da shuwagabannin Fulani na ci gaba da tuntunbar juna domin baiwa Fulanin da aka raba da Muhallansu a jihar Filato izinin komawa gidajensu yayin da ake gab da shiga watan Azumi na Ramadan.

A halin yanzu dai da dama daga cikin Fulanin sun koma gidajen nasu a yankunan kanannan hukumomin Riyom da Barkin Ladi saboda abin da suka kira mawuyacin hali da suke ciki a sansanonin da aka ajiye su.

Sai dai hukumomi sun ce ba su basu izinin komawa a hukumance ba.

Yanzu dai Rundunar tsaro ta musamman mai aikin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato ta bayyana cewa tana tuntubar hukumomin tsaro dake Abuja babban birnin kasar domin duba yiwuwar baiwa Fulanin izini komawa gida.

Karin bayani