Bakassi: Majalisar Najeriya ta nemi a daukaka kara

Taswirar Bakassi Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Bakassi

Majalisar Wakilai ta Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar da ta gaggauta daukaka kara game da hukuncin da wata kotun kasa-da-kasa ta yanke game da yankin Bakassi mai arzikin mai bayan wata takaddama da Najeriyar ta yi da kasar Kamaru a kan yankin.

Hukuncin kotun dai ya mika yankin ne ga kasar ta Kamaru a cikin watan Agustan shekara ta 2008.

Majalisar ta bayyana cewa kasar na da hujjojin da za ta kafa wajen tabbatar da cewa yankin mallakarta ne tun asali.

A watan Oktoba mai zuwa ne wa'adin da aka baiwa Najeriyar na shekaru goma don daukaka kara zai cika.

’Yan Majalisar, musamman wadanda suka fito daga yankunan da ke makwabtaka da yankin na Bakassi, sun bayyana cewa a irin mu’amalar da suke yi da al’ummar yankin ba su taba jin wadanda suka ce da sonsu ne aka mika yankin ga kasar Kamaru ba.

A cewar Ogbonna Nwuke, “Al'ummar Bakassi na Allah-Allah su kasance a bangaren Najeriya. Kuma mun yi mamakin yadda gwamnatin Najeriya za ta mika wani sashenta a daidai lokacin da kasashen duniyar da suka san abin da suke yi ke dagewa wajen tattalin al’ummominsu da kuma fadin kasarsu”.

Ganin cewa gwamnatin kasar ta Najeriya ta riga ta sanya hannu a kan yarjeniyar mika yankin ga kasar Kamaru tun a shekara ta 2006 bayan hukuncin da Kotun kasa-kasar ta yi, dan majalisar ba ya ganin cewa bakin alkalami ya riga ya bushe?

“Muna da hujjar kafawa, saboda bisa tarihi yankin Bakassi mallakinmu ne. A yanzu haka a yankin akwai kayan tarihin da ke nunawa karara cewa yankin Bakassi bangaren Najeriya ne”, inji Mista Nwuke.

Wata madafar da ’yan majalisar ke ganin cewa kwakkwara ce ita ce zargin da suke yi cewa gwamnatin Najeriya ba ta nemi amincewar majalisar dokokin ta wancan lokacin ba kafin ta rattaba hannu a kan yarjeniyar mika yankin ga kasar Kamaru.

A ranar 10 ga watan Oktoba ne dai wa'adin da shara’a ta bai wa Najeriya don daukaka kara game da wannan hukuncin na mika yankin Bakassi ga kasar kamaru zai cika, kuma wannan ya sa wadansu na ganin cewa lokaci ya so ya kure wa gwamnatin Najeriya, amma ’yan majalisar sun ce ba maganar makara a ciki ko da abin da ya rage bai wuce mako guda ba.

Kawo yanzu dai babu wani martanin da ya fito daga bangaren zartarwar gwamnatin tarayya dangane da wannan matsayi na Majalisar.

A ranar 10 ga watan Oktoban shekarar 2002 ne dai Kotun Kasa-da-kasa da ke Hague ta yanke hukuncin da ya mika wa kasar Kamaru yankin Bakassi.

Majalisar dokokin dai ta zargi gwamnatin Najeriya ta wancan lokacin da saurin mika wuya wajen yin na’am da hukuncin kotun; a cewarta gwamnatin ta yi haka ne kawai don ta faranta wa wadansu kasashen duniya da nufin neman suna.