Mayar da Mrs Orunma Oteh ya janyo cece - kuce

Shugaba Goodluck Jonathan Najeriya
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan Najeriya

A Najeriya, wata takaddama na neman kaurewa tsakanin majalisar wakilan kasar da kuma bangaren gwamnati dangane da makomar shugabar Hukumar hada-hadar kudin kasar, Mrs Arunma Oteh.

A jiya ne dai shugaban kasar Goodluck Jonathan ya bayar da umurnin mayar da Mrs Oteh kan kan mukaminta bayan da aka dakatar da ita bisa zargin aikata almandahanar kudi.

A halin da ake ciki dai majalisar wakilan ta ce dole ne a sauke ta daga mukamin bisa zargin cewa ba ta cancanci kujerar baWasu 'yan majalisar ma har sun yi barazanar gurfanar da shugaban kasar gaban kuliya idan ba sauke ta ba.