'Yaran da ke zuwa makaranta sun karu'

Image caption Wadansu yara a makaranta

Wani sabon bincike da kungiyar agaji ta Save the Children ta gudanar ya ce an samu matukar karuwar kananan yara da ke zuwa makaranta a sassa daban-daban na duniya.

A cewar kungiyar, an sake samun raguwar yawan jariran da ke mutuwa.

Sai dai rahoto, wanda kungiyar ta fitar ranar Alhamis, ya ce an samu matukar karuwa a yawan yaran da ke fama da yunwa a kasashen da ke fama matsanancin talauci.

Kungiyar ta yi kira ga Firayim Ministan Burtaniya, David Cameron, da ya yi amfani da wani taron da aka shirya a kan matsalar yunwa, wanda za a yi a lokacin wasannin Olympics, wajen fito da matsalar rashin samun abinci mai gina jiki da kuma yadda za a magance ta.

Karin bayani