Rasha da China sun hau kujerar naki kan Syria

Kwamitin tsaro na MDD kan Syria Hakkin mallakar hoto AFP

Fada na kara kazanta a Damascus babban birnin Syria, a yayinda kokarin diplomasiyya na baya bayannan don kakabawa gwamnatin Assad takunkumi ya kara cin karo da cikas.

Jakadiyar Amurka a majalisar dinkin duniya, Susan Rice ta ce Amurka na kokarin aiki ba tare da kwamitin tsaro na majalisar duniya duniya ba, don karawa kasar matsin lamba.

A cewarta Rasha da China sun hau kujerar naki akan matakin da aka nemi dauka akan Syria'r.

A cewar Rasha kudurin wanda kasashen yammacin duniya ke goyon baya, zai sa a dauki matakin soji akan kasar ne kawai.

Da yake jawabi a birnin na Damascus dangane da hare-haren, shugaban tawagar masu sa-ido da Majalisar Dinkin Duniya ta tura zuwa kasar, Manjo Janar Robert Mood, ya ce yadda zubar da jini ke kara yawaita a kasar na nuna cewa ba ta hau turbar samun zaman lafiya ba.

Janar Mood, wanda ke magana kwana daya kafin karewar wa'adin aikinsa a kasar ta Syria, ya ce tawagar ta Majalisar Dinkin Duniya za ta yi tasiri ne kawai idan shirin sasantawa a siyasance ya fara, kuma ya yi Allah-wadai da hare-haren da aka kai ranar Laraba.

''Ina kuma aikewa da ta'aziyyata da kuma nuna tausayawata ga iyalan dukkanin wadanda suka mutu da kuma wadanda suka samu raunukka a harin da aka kai ranar Laraba. Ina bayyana bacin raina game da harin kuma ina kira ga bangarorin da ke fadan da su kawo karshen zubar da jini da tashin hankali ta kowacce fuska, su kuma mayar da himmarsu wajen warware wannan rikicin cikin lumana”, inji Janar Mood.

Wata ’yar kasar ta Syria wadda ke yiwa wata kungiyar ’yan tawayen kasar aiki, Rafif Jouejati, ta ce sun damu ainun cewa gwamnati ta fara ramuwa ne a kan kisan mutanen uku.

“Abin da muke gani a Damascus yanzu sakamako ne na rudanin da Bashar al-Assad ya shuka a ko’ina a cikin Syria, kuma abin da muke tsoro yanzu shi ne wadansu daga cikin kungiyoyin mayaka ko Shabiha wadanda ke goyon bayan gwamnati sun karbe fadan a hannayensu.

“Muna jin rahotannin cewa kungiyoyin na Shabiha na bi unguwa-unguwa a birnin Damascus suna kar-kashe mutane”, inji ta.

Gwamnatin Amurka dai ta ce kisan manyan jami'an tsaron na Syria na nuna cewa ikon kasar ya fara subucewa daga hannu Bashar al-Assad.

Sai dai gwamnatin ta Syria ta ce tana fatattakar wadanda ta kira kungiyoyin ’yan ta'adda ne da wadannan sababbin hare-haren da take kaiwa.

Karin bayani