Tilas ne Habre ya fuskanci shari'a: Inji ICC

Hissene Habre, tsohon shugaban kasar Chadi Hakkin mallakar hoto
Image caption Hissene Habre, tsohon shugaban kasar Chadi

Dazu -dazun nan ne kotun duniya dake birnin Hague ta yanke hukuncin cewa dole ne tsohon shugaban kasar Chadi Hissené Habré ya fuskanci sharia a kasar Senegal.

Kotun ta ce ya kamata a yi hakan ba tare da wani bata lokaci ba, kuma idan baa yi hakan ba, to ya kamata a tesa keyarsa zuwa kasar Belgium domin ya fuskanci shari'a.

Ana zarginsa ne da aikata laifuffuka masu dimbim yawa da suka hada da keta hakokin bil'adama da kuma gallazawa fiye da mutane dubu goma wadanda suka nuna adawa da gwamnatinsa.

A wani labarin kuma, lauyoyin tsohon Shugaban Liberia, Charles Taylor, sun daukaka kara game da samunsa da laifi da kuma hukuncin da aka yanke masa dangane da laifukan yaki.

A cikin watan Afrilu dai aka samu Mr Taylor da laifin taimakawa da kuma goyon bayan yan tawaye a yakin basasar Saliyo.

Karin bayani