Za a yanke hukunci a kan Hissene Habre

Hakkin mallakar hoto
Image caption Hissene Habre

A ranar Juma'a ne Kotun Duniya za ta yanke hukunci a kan ko ya kamata kasar Senegal ta tasa keyar tsohon shugaban kasar Chadi Hissene Habre domin ya fuskanci tuhuma a kasar Belgium.

Ana zargin Mista Habre ne da laifin azabtarwa da kisan dubban masu adawa da shi lokacin da ya mulkin kasar a shekarun 1980.

A yanzu haka dai yana zaman daurin-talala ne a kasar ta Senegal, wurin da yake gudun hijira.

Harwayau, Kotun za ta yanke hukunci ko ya kamata Mista Habre ya gurfana a kasar ta Senegal.

Karin bayani