Dubban 'Yan Syria na barin kasar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani dan tawaye a Syria

Dubban 'yan Syria na ficewa daga Damascus babban birnin kasar, inda 'yan tawaye ke kokarin kifar da gwamnatin shugaba Assad.

Mutane kusan dubu talatinne aka bada rahoton cewar sun tsallake zuwa makwabciyar kasar wato Lebanon, amma hukumar kula da 'yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta ce adadin bai wuce mutane kusan dubu takwas da dari biyar ba

. Kakakin hukumar ta ce wasu mutannen suna gudu zuwa kasashen Jordan da Turkiya da kuma Iraki.

Haka zalika, wasu 'yan Armenia sun fice daga Syria, duk da cewar sun dade suna zama a kasar tun iyaye da kakkanni.

Ana ci gaba da gwamza fada a Damascus, a yayinda aka bada rahoton cewar dakarun gwamnati sun kara kwace gundumar Midan, sannan kuma suna kara tsaurara kai hare hare a yankin gabashin Jubar.

A daren jiya dai, mayakan 'yan tawaye sun kwace ikon kan iyakar Syria da kasar Iraki, da kuma mahadar kasar da Turkiya.

Harin da aka kai wa 'yan Israela ya dagula lamura

Wani abu da masana ke ganin zai dagula lamura a yankin Gabas ta Tsakiya, baya ga rikicin Syriar, shi ne harin da aka kai wa wasu 'yan Israela a Bulgaria.

Harin dai ya yi sanadiyar mutuwar 'yan Israela guda shida.

Ita dai Israela tana zargin kungiyar Hezbullah ta Lebanon da kuma Iran da kai harin.

Masana harkokin tsaron Israela sun yi imanin cewa, wannan shi ne hari na baya- bayan nan -kuma na farko wanda ya yi nasara- a cikin jerin hare-haren da kungiyar Hezbullah ke kai wa yahudawa a fadin duniya.

Harin na Burgas ya sanya Israela ta kara fadawa cikin wani sabon cece-kuce.

Haka kuma, harin zai kara tashe-tashen hankula uku da da ma ake yi a yankin; watau zai motsa tsohuwar gabar da ke tsakanin Israela da Hezbollah a kudancin Lebanon; sannan zai kara dagula rikicin kasar Syria; kana zai rura-wuta rikici da ke ci tsakanin Israela da Iran musamman dangane da batun shirin nukiliyar kasarta Iran.

Karin bayani