Ana yi wa mutanen da aka kashe a Norway addu'a

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Anders Behring Breivik

A ranar Lahadi ne ake gudanar da addu'o a sassa daban-daban na kasar Norway don tunawa da mutane 27 da wani dan bindiga, Anders Behring Breivik, ya kashe shekara daya cif kenan.

Yawancin wadanda suka mutu matasa ne da ke halartar wasu shagulgulan shakatawa na bazara a tsibirin Utoya.

Sauran kuma sun mutu ne a wani harin na bam da aka dana a wasu ofisoshin gwamnati da ke Oslo, babban birnin kasar.

Brevik, wanda ya dauki alhakin kisan mutanen, ya ce yana kare kasar ta Norway ne daga mamayar da musulmi ke yi mata.

Karin bayani