Masar: dan majalisa ya aikata lalata

Hakkin mallakar hoto none
Image caption 'Yan mata a masar

An samu wani dan majalisar Misra mai kaifin ra'ayin Islama da aikta lalata a bainar jama'a

Wata kotu a Misran ta same shi ne da laifi kan wani zargi da ake masa na yin lalata da wata a cikin motarsa.

Tun da farko dan majalisar ya ce, ba wani batun lalata da ya shiga tsakaninsa da matar kuma ma 'yar dan uwansa ce. Amma kunyar yin hakan ta sa ya shiga buya.

Ana dai ganin wannan shari'a a matsayin wata abar kunya ga 'yan Salafiyya-wadanda suka nemi da a tsaurara hana hulda tsakanin maza da matan da ba 'yan uwan juna ba ne.

An yankewa dan majalisar, mai suna Ali Wanis, hukuncin daurin watanni sha takwas a gidan kaso akan kama shi da aka yi a halin da bai kamata ba da wata daliba.