Ana bincike a gidan James Holmes

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jami'an tsaro na kokarin shiga gidan Holmes

Ma'aikatan Hukumar Leken Asirin Amurka, FBI na binciken kayayyakin James Holmes, mutumin da ya harbe wadansu mutane a lokacin da suke kallon fim a gidan sinima da ke Denver na jihar Colorado.

Ma'aikatan sun ce suna gudanar da binciken ne domin gano ko akwai wata shaida da ka iya bayar da haske kan dalilan da suka sanya mutumin, James Holmes, ya bude wuta kan masu kallon fim a ranar Juma'a da safe, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 12, kana wasu da dama suka jikkkata.

Maikatan FBI da 'yan sanda da kuma kuma ma'aikatan kashe gobara sun kwashe kwanaki biyu suna aiki ciki nutsuwa kafin su tsara yadda za a iya shiga gidan Mista Holmes, inda ya makalkala wasu abubuwan da ke fashewa.

An yi amfani da wani mutum-mutumi da ke aikin kwance bama bamai wanda ya warware wayoyin da da Mista Holmes ya zagaye gidan da su.

'Yan sanda sun ce wayoyin nade suke da wasu abubuwa da ke fshewa, kuma da a ce wani ya taba su kafin lokacin, da gidan ya yi rugurugu ta yadda abubuwan za su iya kashe makwabtan mutumin.

Karin bayani