An kashe Indiyawa a Maiduguri

Image caption Taswirar Najeriya

A najeriya rahotanni daga birnin Maiduguri a jihar Borno na cewa wasu da ba a san ko su wanene ba sun kashe wasu mutane biyu 'yan kasar Indiya yayin da kuma aka jiwa mutum na uku mummunan rauni.

Lamarin dai ya faru ne yau da safe a wani kamfanin sarrafa karo dake Maidugurin inda 'yan kasar ta India ke aiki.

Wata sanarwa daga kakakin rundunar tsaro ta musamman dake Miadugurin, Laftanar Kanar Sagir Musa yace, lamarin ya auku ne da misalin karfe goma na safe yayin da ake tafka ruwan sama.

Sanarwar ta kuma ce, wadanda suka kai harin sun yi awon gaba da kudi naira dubu casa'in.

Ya zuwa yanzu ba wasu da suka dau alhakin kai wannan hari.