'Yan sandan Najeriya na taimaka wa wajen tabarbarewar tsaro'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sandan Najeriya

A Najeriya, kungiyar samar da fahimta tsakanin 'yan kasar da 'yan sanda na zargin wasu daga cikin 'yan sandan da hannu wajen tabarbarewar tsaro a kasar.

'Yan kungiyar, wacce a takaice ake kira PCRC sun ce wadansu 'yan sandan na kawar da kai daga ayyukansu ko da kuwa an kai musu rahoton aikata wani laifi.

Wani jami'in kungiyar, Alhaji Chief S.B Ogunlanu, ya shaida wa BBC a jihar Rivers cewa a lokuta da dama suna kai wa 'yan sanda bayanai game da faruwar wani laifi, amma ba za su je wajen don magance matsalar ba.

Kazalika, Alhaji Ogunlanu ya zargi 'yan sandan da hada-kai da masu aikata laifuka.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sanda ta jihar, ASP Ben Oyagunan, ya musanta zargin, yana mai cewa 'yan sandan na gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

Karin bayani