Gyaran kundin tsarin mulkin Najeriya

Taswirar Najeriya
Bayanan hoto,

Taswirar Najeriya

A Najeriya, wani kwamitin majalisar dattawan kasar ya kammala wani zama don rairaye bukace-bukacen al'uma da ya shafi gyara ga kundin tsarin mulkin kasar.

Cikin batutuwan da ya hada har da bukatar kayyade wa'adin mulkin shugaban kasa da na gwamnoni zuwa zango daya mai tsawon shekara biyar.

Sai dai kwamitin ya ce majalisun dokokin jihohi da sauran wadanda abin ya shafa su ma suna da hurumin bayyana nasu matsayin kafin a aiwatar da gyare-gyaren.