Obama ya ziyarci Colorado

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaba Obama

Shugaba Obama ya je Colorado domin ya gana da jama'a da 'yan uwan wadanda harbin kan mai tsautsayin da aka yi a wata silima a garin Aurora ranar juma'a ya ritsa da su.

Mr Obama zai ziyarci wasu daga cikin wadanda suka ji raunuka, zai kuma gana da iyalan da suka rasa 'yan uwansu.

Har yanzu mutane tara na kwance hajaran majaran bayan harin da wani dan bindiga ya kai inda ya kashe mutane goma sha biyu.

Magajin garin birnin New York, Micheal Bloomberg, ya yi kira ga shugaba Obama da abokin hamayyarsa, Mitt Romney da su dauki mataki kan rage yawan bindigogi a hannun jama'a.