An kama sojojin da ake zargi da bore a Madagascar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutiny in Madagascar

Sojojin Madagascar sun kai farmaki kan wani sansani dake daura da filin jirgin saman kasar, inda suka kama wadansu da ake zargi da haddasa boren soji a kasar.

Mutane uku ne suka mutu a farmakin ciki har da wanda ake zargi da jagorantar boren da kuma wani kyaftin din soja da aka tura shi domin tattaunawa da sojojin da suke boren.

Ba a dai tantance manufar sojojin da suka yi boren ba, amma dai yunkirin juyin mulkin da suka yi na zuwa ne daf da wata ganawa da za'a yi ranar Laraba domin sasanta rikicin siyasar da kasar ke ciki.

Ana jayayya ne tsakanin wasu mutane biyun da kowannensu ke da'awar shine shugaban kasar tun bayan hambararda tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana shekaru uku da suka wuce.

Karin bayani