'Yaran Syria miliyan biyu na cikin hadari'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu yara a Syira rike da makamai tare da manya

Wata kungiyar agaji ta Birtaniya mai kula da kare hakkin yara a lokacin yaki, War child, tayi gargadin cewar rayukkan yara miliyan biyu dake birnin Damascus na cikin hadari, a yayinda fada ke kara tsananta a babban birnin na Syria.

A cikin wani cikakken rahoton da ta fitar kan yadda fadan ya shafi kananan yara, kungiyar tace ana aikata kowane daya daga cikin ababe shidan da Majalisar dinkin duniya ta hana a aikatawa yara a lokacin yaki.

Abubuwan dai sun hada da kisa, da nakasawa, da tilastawa yara aikin soja, da fyade, da sacewa da kuma kai hare-hare kan makarantu da asibitoci.

War Child ta ce gaba daya bangarorin da ke yaki da juna a Syria na kai hare-haren da suka hada da kisan gilla, da munanan raunuka tare da fyade kan kananan yaran.

Karin bayani