Turai za ta sassauta wa Zimbabwe takunkumi

Robert Mugabe Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince ta sassauta takunkumin da ta kakabawa kasar Zimbabwe.

Tun shekaru goman da suka wuce ne dai aka kakabawa kasar takunkumin a matsayin martani ga keta hakkokin bil-Adama da tashe-tashen hankula na siyasa.

A cewar Kungiyar ta Tarayyar Turai, za ta jingine takunkumin da ta kakabawa Zimbabwe da zarar an gudanar da sahihin zaben raba-gardama a kan sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Mai yiwuwa a gudanar da zaben raba-gardamar kafin karshen wannan shekarar.

Za a yi sassaucin ne dai a kan akasarin daidaikun 'yan Zimbabwe su dari da goma sha biyu, da kuma cibiyoyin da har yanzu Tarayyar Turan ta haramtawa tafiye-tafiye zuwa kasashenta ta kuma hana su taba kadarorinsu.

Sakataren Harkokin Wajen Burtaniya, William Hague, ya ce Tarayyar Turan na duba yiwuwar daukar matakin da ya dace da ci gaban da aka samu na zahiri.

Mista Hague ya kuma ce za a ci gaba da nazari a kan wannan mataki, kuma idan abubuwa suka kara lalacewa to Tarayyar ba za ta yi wata-wata ba za ta mayar da martanin da ya dace.

Sai dai kuma ministocin harkokin wajen Tarayyar sun tsaya kai-da-fata cewa a daidai wannan lokaci ba za a janye takunkumin da aka kakabawa Shugaba Mugabe da makusantanshi ba.

Magoya bayan Mista Mugabe dai sun dade suna godon a janye takunkumin ba tare da gitta wani sharadi ba, suna masu cewa takunkumin ya yi mummunan tasiri a kan tattalin arzikin kasar ta Zimbabwe.