Kotu ta ce a wallafa neman mai wasu kudi dake tababa a kai

James Ibori Hakkin mallakar hoto PA

Wata kotu a Abuja ta debarwa Hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'anati watau EFFC wa'adin kwanakin bakwai da ta wallafa bayanai a cikin jaridu na neman duk wani dake ikirarin cewa shi ne ya mallaki wasu kudade da ake takaddama akai da yawansu ya kai dala miliyan goma sha biyar .

Haka kuma gwamnatin kasar ta nemi kotun da ta mika mata wadannan kudaden saboda a cewar ta basu da wani amfani a inda suke ajiye.

Kudaden dai tun lokacin tsohon shugaban hukumar EFFC , Malam Nuhu Ribadu ne suke , lokacin da ya zargi tsohon gwamnan jihar Delta James Ibori da ba shi toshiyar baki a tuhumar da aka yi masa a shekerar 2007.