Ana cigaba da neman gawarwaki a ambaliyar Jos

Image caption Taswirar Najeriya

Jami'an bayarda agajin gaggawa a birnin jos na tsakiyar Najeriya sun ce suna ci gaba da kokarin gano dimbin mutanen da har yanzu ba a gansu ba kuma ba a gano gawawwakinsu ba, bayan da wata ambaliyar ruwa mai karfi ta afkawa yankunansu ranar litinin.

Hukumomin Nijeriyar sun ce fiye da mutane 3000 ne ambaliyar ta raba da muhallansu yanzu haka tare da rushe gidaje fiye da gidaje 200.

Unguwannin da ambaliyar ta fi muni dai sun hada da Gangare, da Rikkos, da Unguwar Rogo da yankin Ali Kazaure da kewayensu inda kungiyoyin agaji suka ce mutane kimanin arba'in ne suka rasa rayukansu kuma wasu kwatankwacin haka sun bata.

Wakilin BBC a Jos yace ruwan ambaliyar dai ya sha kan gidaje da dama a wadannan unguwannin— wadansunsu sun ruguje baki daya; kuma ruwan mai toroko ya kuma yi awon gaba da dukiya mai dimbin yawa.

Karin bayani