Kusan mutane arba'in ne suka halaka a Jos

Ambaliyar ruwa a Jos Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ambaliyar ruwa a Jos

Bayanai dai na ci gaba da fitowa fili game da girman ta’adin da mummunar ambaliyar ruwan ta yi al’umomin na birnin Jos inda adadin mamata sannu a hankali ke karuwa.

Sakataren kungiyar agaji ta Red Cross a jihar Filato, Mista Manaseh Pampe, ya shaida mani cewa sun tabbatar da mutuwar mutane talatin da tara ne izuwa maraicen jiya, yayin da wani jami;I a reshen ayyukan agaji na kungiyar Jama’atu Nasril Islam ya gaya mani cewa a yau ma sun yi wa wasu Karin gawawwaki biyu jana’iza.

A nagaren guda kuma hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu da kuma daidaikun mutane masu hannun baiwa sun fara taimakawa wa wadanda ambaliyar ta raba da muhallansu wadanda wasunsu ke zaune a sansanoni, wasu kuma sun raba a gidajen yan uwa da abokan arziki.

Na ziyarci daya daga cikin sansanonin, inda na tarar ana raba kayakin da hukumar bada agajin gaggawa ta Nijeriya wato Nema ta bayar, da suka hada da barguna, da kayan abinci da da tufafi kuma na zanta da wasu daga cikin mazauna sansanin.

To sai dai kuma tuni gwamnatin jihar ta Filato ta kafa wata tawaga ta musamman domin ziyaratar al’umomin da bala’in ya shfa da nufin jajanta masu.

Na tambayi shugaban tawagar kana kwamishian albarkatun ruwa na jihar, Malam Idi Waziki, ko shin mene ne ya sanya kawo yanzu gwamnatin bada taimako ga wadanan ambaliyar ta shafa ba?

Hukumar agajin ggagawa ta Nijeriya wato NEMA dai, ta bayyana cewa gidaje fiye da dari biyu ne ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kamar bakin kwarya ta ruguza, mutane fiye da dubu uku suka rasa mazaunansu, yayin da wasu mutane fiye da talatin kuma ba a gansu ba sama ko kasa tun bayanda ambalkiya ta rutsa da su, amma dai hukumomi cewa suke yi basu dakatar da aikin ceto ba.

Karin bayani