An bindige malamin addinin musulunci a Kano

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Taswirar Najeriys

Rahotani daga birnin Kano na arewacin Najeriya sun ce wasu 'yan bindiga sun hallaka wani malamin addinin musulunci jiya da dare.

Malam Shuaibu Gwamaja ya hadu da ajalisansa ne lokacin da ya dawo daga masallaci bayan yin sallar Isha'i.

A cewar majiyar 'yan sanda da kuma ta mazauna unguwar da lamarin ya faru dai, wasu mutane ukku ne suka zo a cikin mota suka tsaya kofar gidan malamin jim kadan bayan ya dawo daga sallar Isha'i; inda suka aika aka sallamoshi kuma zuwansa ke da wuya sai suka bude masa wuta abin da yayi sanadiyyar mutuwar sa nan take.

Daya daga cikin mazauna unguwar da abin ya faru wanda bai amince a baiyana sunansa ba da ya zanta BBC, yece ba su da masaniyar ko su wa ne suka kashe wannan malamin da kuma ko menene dalilinsu ba.

Zama cikin tsoro

Sai dai yace lamarin ya jefa tsoro cikin zukatan galibin mazauna unguwar abin da yasa duk suka shisshige gidajen su tun da wuri domin gudu abin da ka iya biyowa baya.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jahar Dsp Ridwanu Muhammad Dutse, yace malamin kadai ne aka kashe a cikin wannan harin faru da misalin karfe takwas da rabi na dare.

Dsp Ridwan yace amma 'yan sanda basu samu kama ko daya daga cikin makasan ba a daidai lokacin da muke zantawa dashi koda yake yace sun shiga farautar su.

Garin na kano dai na daya daga cikin wurarenda ke fama da hare-haren bindiga da bama-bamai a kan daidaikun mutane da kuma ofisoshin jami'an tsaro tun a farkon wannan shekarar.

Karin bayani