Ana ci gaba da gumurzu a Damascus da Aleppo

Mayakan Syria a tankokin yaki
Image caption Mayakan Syria a tankokin yaki

Wani wakilin BBC a wajen Aleppo, birnin na biyu mafi girma a Syria, ya ce jiragen saman yaki sun kai hare haren bam a yankin gabas na birnin. Wakilin na BBC ya ce hakan alamu ne na kara ta'azzarar wannan rikici.

Ana kai hare bharen ne yayinda mazauna birnin Aleppo da wasu masu adawa da gwamnati ke cewa wasu mayakan 'yan tawaye sun kaddamar da wani hari a kokarin sake karbe iko da wasu unguwani na marasa galihu.

Masu fafutuka sun ce fursunoni sun yi tarzoma a manyan gidajen yarin kasar biyu a biranen Homs da Aleppo, suna masu cewar suna fargabar za a aiwatar da kisan kare dangi a gidajen yarin, yayinda dakarun tsaro ke barazanar kai masu farmaki.

Akwai rahotannin dake cewa dakarun gwamnati sun murkushe boren fursunonin a birnin Aleppo.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da zata tabbatar da gaskiyar labarin.

A waje daya, Praministan Turkiyya na cewa al'ummar Syriar na dab da kawo karshen wannan tashin hankali.

Karin bayani