'An kashe Mutane 9 cikin boren fursuna a Syria'

Hakkin mallakar hoto none
Image caption Wasu 'yan tawayen Syria a birnin Aleppo

'Yan tawayen kasar Syria sun ce an samu boren Fursuna a gidajen kurkukun da ke a biranen Aleppo da Homs.

Masu fafutukar sun ce akalla mutane 9 ne aka kashe a boren kurkukun Aleppo kuma su na fargabar adadin zai karu bayanda jami'an tsaro suka fara shirin kai hari kan gidaje yarin dake biranen biyu.

A nasa bangaren gidan talabijin na gwamnatin Syria ya nuna wuraren da aka yi barna a kudancin birnin Damascus da kuma gawarwakin wasu mutanen da yace sojojin haya ne daga kasashen waje.

Gidan talabijin din ya kuma ce dakarun gwamnati sun kwace ikon sassan da 'yan tawayen suka karbe a makon jiya.

Karin bayani